Ga Amarya ga Wanda ta nuna
Karaso ango dawisu Ka zauna
Yau Amarya tazam mallakin Ka
Gimbiya za tai mulki a gidan Ka
Mance Kowa Kula da abarka
Mance komai Ka jata Jikin Ka
Kai take so kar ka so fushin ta
Murmusa Nutsuwar Ka na wajen ta
Shalelen Ango ta farko ku gan ta
Kyakkyawa damuwar Sa damuwar ta
Faruk Bala Ahmad Ka rabauta
Kayi mata wacce ba ruwan ta
Farida Yakubu barakallah ta Ka
Tantabara da angan ta za’a gan Ka
Rabo ya rantse munafukai ku gane
Auren soyayya Wannan mukaddari ne
Kwarya ta bi kwarya wance tabi wane
Naga masoya da yawa ku dabanne
Lokacin ku ya yi ku ma’aurata ne
Kin girmi wance ya girmi wane
Kin girmi wance ya girmi wane
Faruk Bala Ahmad Ka rabauta
Kayi mata wacce ba ruwan ta
Farida Yakubu barakallah ta Ka
Tantabara da angan ta za’a gan Ka