LyricFind Logo
LyricFind Logo
Profile image icon
Lyric cover art

FARKO (beginning)

Apple Music logo
Deezer logo
Spotify logo
Lyrics
Malam6ix
Wayyo
Yeh yeh

Allah ya bani kyauta ayau
Wacce tanada kima da kyau
Kallon ta ke tsinka mun miyau
A ganin farko
Na samu mata Raina fayau
Hankali na a kwance kalau
Jiki na Babu nauyi sayau
Yau Daren farko
Suna nawa an canza min
Malam6ix ango ake ce min
Ku kalli yadda dangi ke min
Gatan farko
Hawaye mama kin share min
Abba girma na ka danka min
Kadau dawainiya ka yi min
Yadda Zan karko

Umma na gode
Abba Na gode
Kun yi min aure
Tudu na haure
Sa'a na kere
Kuma na more
Ban iya biyan hakkin ku
Duk Ina son ku Kun saya mun gado

Wata shida Zan Yi ba na fita
Ina da Mai Yi min fifita
Ba Mai gani na in ba ita
So zai yi danko
Ba kishiya Zan Mi ki ba
Ba kuma zana canza ki ba
Bacin riba na samu riba
Ke da na dauko
Na samu duniya na sani
Auren ki Babu Danasani
Ko Babu kwalliya kin mini
Matar farko
Komai aka ce Da ni na rike
Ban sakaki bare in sake
Wannan inuwa na fake
Namijin farko

Umma na gode
Abba Na gode
Kun yi min aure
Tudu na haure
Sa'a na kere
Kuma na more
Ban iya biyan hakkinku
Duk Ina son ku Kun saya mun gado

Umma ta hadan babban biki
Ranar naira ta ji jiki
Ga surukai yau ga siriki
Sun tattako
Ko ina na duba koina
Ban ganin kowa Sai baby na
Mai dariya da kyan magana
Sa'a na tako
Masu son auren ki na bibbige
Na murkushe su na daddage
Ba rangwame bare in rage
Son da na dauko
Du'a'in da al'uma ke Mana
Ya rabbana ka amsa Mana
Kada maziga su Bata Mana
Kaunar farko

WRITERS

SULAIMAN SAEED

PUBLISHERS

Lyrics © O/B/O DistroKid, Sentric Music

Share icon and text

Share


See A Problem With Something?

Lyrics

Other

LyricIQ Analysis

Top Emotion

Enjoyment

Sentiment
Thumbsup IconThumbsup IconThumbsup Icon
Theme

Sexual